Attajiran Ƙasar Nan Sun Yiwa Super Eagles Alƙawarin Maƙudan Kuɗaɗe

0 200

Manyan Attajiran ƙasar nan guda biyu, Aliko Dangote da Femi Otedola sun yiwa ƴan wasan tawagar Super Eagles ɗin ƙasar nan dake gasar cin kofin Afirka a Masar alkawarin kuɗaɗe idan sun samu nasara a sauran wasannin su guda biyu da suka rage, bayan nasarar da suka samu a wasan daf da na kusa da na karshe kan Afirka ta kudu.

Yayin ziyarar da suka kaiwa ƙungiyar a otel ɗin da suke a Birnin Alkahahira, Aliko Dangote yayi alƙawarin biyan Dala 50,000 kan kowanne ƙwallo guda da ƙungiyar ta jefa a wasannin da za suyi nan gaba, yayin da Femi Otedola yayi alƙawarin Dala 25,000 kan kowanne ƙwallo guda.

Kafin wannan alƙawarin, wani attajirin a ƙasar nan mai harkar mai, Captain Hosea Wells Okunbo ya yiwa kowanne ɗan wasa guda alƙawarin Dala 20,000 idan sun doke kamaru kuma ya biya su bayan nasara da suka samu, kana shima Gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu ya baiwa kowanne Dan wasa Dala 5,000 saboda gagarumar nasara da suka samu akan Kamaru.

Shi ma kamfanin man AITEO dake haɗin gwuiwa da Hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar nan ta biya Dala 25,000 akan kowanne ƙwallo guda da ƙasar nan ta jefa a wasan Kamaru.

Leave a Reply

%d bloggers like this: