Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC, Felix Morka, ya bayyana cewa duk da ƙaruwar mutane da ke sauya sheka zuwa jam’iyyar, jam’iyyar mai mulki ba ta da niyyar mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya tak.
Ya bayyana cewa a lokacin da Jam’iyyar PDP, ke mulki, ta rike fiye da jihohi 28 ba a zarge ta da ƙoƙarin mayar da ƙasar ta zama ƙasa mai jam’iyya ɗaya ba.
Morka ya ce babu wani laifi ga mambobin jam’iyyun PDP da LP da ke sauya sheka zuwa APC idan suna son su haɗa kai da tsarin jam’iyyar mai mulki.
Ya ce, Da yawa daga cikin waɗannan mutane na shigowa a cewarsu don zama a ɓangaren da ke kan tsari.
A ƙasar mu, duka a cikin ƙundin tsari dokar zaɓe, da kuma sauran dokoki da dama, akwai tsarin da ya tabbatar da cewa Najeriya ƙasa ce mai jam’iyyun siyasa da dama kuma al’umma ce mai ra’ayoyi daban-daban.”
Don haka, ba za mu iya ba a matsayin jam’iyya muyi abin da zai saɓa wa tsarin mulkin ƙasa ba, ta hanyar mayar da ƙasar ma jam’iyya ɗaya.