Gwamnatin jihar Niger ta gano cewa yan fashin dajin dake addabar jihar ba, yan kasar nan bane, wasu bata gari ne dake shigowa jihar daga kasashen dake makwabtaka da Nijeriya.

Tare da bukatar gwamantin tarayya ta taimaka wajan ceto jihar daga hannun wadannan bata garin.

Haka zalika Gwamnan jihar ya hada wata rundunar ta musamman mai dauke da jami’an tsaro, da yan sintiri da suka kai 1000 domin kutsawa dazuka, da wasu maboyan yan bindigar dake fadin jihar.

Haka zalika ya gina wata rundunar ta musamman domin kubutar da daliban islamiyyan nan ta Salihu Tanko Islamiyya dake Tegina, ta karamar hukumar Rafi.

Kafin hakan dai gwamna Bello ya ziyarci iyayen daliban a jiya Alhamis tare da yi musu alkawarin kubutar da yayan nasu cikin kwanciyar hankali.

Kazalika ya yabawa jami’an tsaro bisa irin kokarin da sukeyi wajan yaki da yan bindIga da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa,

tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta riga ta samarwa jami’an tsaro kayan aiki domin gudanar da ayyukan su batare da katsalandan ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: