Ba za mu shiga tsarin daidaita farashin kayayyaki a kasuwanni ba – FCCPC

0 91

Biyo bayan cece-kuce da aka samu game da barazanar da Hukumar Kula da Gasar Kasuwanci da Kare Haƙƙin Masu Sayen Kaya ta Kasa (FCCPC) ta yi na shiga tsakani kan hauhawar farashin kayayyaki, hukumar ta bayyana cewa ba za ta shiga cikin tsarin daidaita farashin kayayyaki a kasuwanni ba.

Wannan dai sabanin wata sanarwa ce da aka danganta ga Mataimakin Shugaban Hukumar, Tunji Bello, a makon da ya gabata, wanda ya ba da wa’adin wata guda ga ƴan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a kasuwanni da suke gallazawa al’umma, yana barazanar su rage farashin kayansu ko kuma su fuskanci fushin hukumar.

Duk da haka, hukumar ta dage cewa za ta aiwatar da dokokin da ke hana dabarun shigo da harkokin rashin gaskiya a kasuwanci, tare da cewa za ta kare haƙƙoƙin masu sayen kaya a fadin kasar.

A wata sanarwa da Ondaje Ijagwu, Darakta na Ayyukan Musamman ya fitar jiya a Abuja, hukumar ta ce, tana nan akan kudurinta na daukar matakin da ya dace wanda ke mutunta dabarun kasuwanci mai ƴanci yayin da kuma take tabbatar da cewa an kare haƙƙoƙin masu amfani da kaya daga munanan dabi’un wasu ƴankasuwar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: