Ba za’a sake barin ‘yan kasa da shekaru 18 su zana jarabawar JAMB ba

0 135

Ministan ilimin Najeriya, Farfeasa Tahir Mamman ya bayyana cewa babu yaron da za a sake bari ya zauna jarrabawar kammala sakandire ba tare da cika shekaru 18 da haihuwa ba.

Farfesan wanda ya bayyana hakan yayin wata zantawarsa da ya yi a ranar Lahadi  gidan talbijin na Channels, ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta umarci hukumomin da ke kula da zana jarrabawar kammala sakandare ta WAEC da WASSCE da NECO da su bi sabon umarnin nata na kasancewar yara ƴan shekaru 18 kafin cancantar zana a jarrabawar.

Ministan ya kuma ƙara da cewa sabuwar ƙa’idar ta shafi  yaran da ke son zana jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare da ake kira UTME da hukumar JAMB ke tsarawa.

Ministan ya yi ƙarin haske dangane da shekarun da ya kamata kowanne yaro ya kwashe a makarantun kafin firamare da na firamare har zuwa kammala sakandare.

Ministan ya yi ƙarin haske dangane da shekarun da ya kamata kowanne yaro ya kwashe a makarantun kafin firamare da na firamare har zuwa kammala sakandare.

Daga ƙarshe ministan ya ce “daga yanzu hukumomin NECO da WAEC ba za su ƙyale duk yaron da bai kai 18 ya zauna jarrabawar kammala sakandare ba.

Ƙungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta fara yajin aikin gargadi na kwana bakwai a dukkanin cibiyoyinta na faɗin ƙasar, inda ta buƙaci a sako Dakta Ganiyat Popoola, mambarsa da ke hannun masu garkuwa da mutane tsawon wata takwas.

Shugaban NARD, Dakta Dele Abdullahi ne ya sanar da fara yajin aikin a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya bayyana cewa za a fara yajin aikin da ƙarfe 12:00 na safe a ranar Litinin 26 ga watan Agusta, 2024.

An yanke shawarar yajin aikin ne a wani taron gaggawa da jagororin ƙungiyar suka gudanar a ranar Lahadi, 25 ga Agusta, 2024.

An sace Dokta Ganiyat Popoola, magatakarda a sashin kula da ido da ke Babban Asitin Ido na ƙasa da ke Kaduna ne, kusan wata 8 da suka gabata, tare da mijinta da kuma ɗan uwanta.

Sai dai an saki mijinta a watan Maris, amma aka ci gaba da riƙe Popoola  din da dan uwanta.

A Makonni da suka gabata, mambobin NARD sun yi zanga-zanga a dukkan manyan asibitocin ƙasar, don neman a gaggauta sakinta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: