Ba zamu dawo da afmani da layukan sadarwa ba sai matsalar yan bindiga ta kare- Gwamnan Tambuwal

0 69

An rufe layukan Sadarwa a wasu Kananan Hukumomi 14 na Jihar Sakkwato, a wani yunkuri na magance matsalar ’yan bindiga a Jihar.

Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake yake tattaunawa da Muryar Amurka a Jiya Litinin.

Gwamna Tambuwal ya ce an samu amincewar gwamnatin tarayya kafin katse Layukan Sadarwar, inda ya kara da cewa an rufe hanyoyin sadarwar ne a kananan hukumomi da suka fi fuskantar barazanar hare-haren yan bindiga.

Gwamnatocin Jihohin Katsina da Zamfara sun dauki matakan sauke hanyoyin sadarwa a Jihohin su.

Gwamnan ya ce rufe layukan sadarwa da sauran matakan da aka dauka a Zamfara, ya sa bata-garin kutsawa zuwa wasu sassa na Jihar Sakkwato, suna garkuwa da mutane tare da kashe wasu.

Kazalika, ya ce yankunan da aka katse layukan sadarwa a jihar sun hada da guda 10 wadanda Dajin Rugu matattarar ’yan bindiga ya ratsa ta cikinsu, da wasu uku da ke da iyaka da jihohin Zamfara da Kaduna, wadda ita ma bata-garin sun addabe ta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: