Ba zan iya janyewa akan takara ta ba sai abin da Shugaba Buhari ya ce – Gwamna Badaru

0 64

Gwamnan Jihar Jigawa Badaru Abubakar ya ce idan Sugaba Muhammadu Buhari bai amince da shawararsu ta ba wa ‘yan takarar kudancin Najeriya tikitin takarar shugaban ƙasa na APC ba dole su janye.

Badaru ya faɗa wa BBC Hausa cewa ya yi mamakin ganin takardar da ta karaɗe shafukan zumunta cewa an amince da matasayin gwamnonin Arewa na miƙa wa ɓangaren Kudu takarar, yana mai cewa shawara ce kawai.

“Haƙiƙanin gaskiya shawara ce za a kai wa baba [Buhari], idan ya amince a ɗauki wannan mataki, idan bai amince ba kuma a ci gaba da shawarar da ya bayar tun da dukkanmu gwamnonin Arewa masu biyayya ne gare shi,” a cewar gwamnan wanda shi ma mai neman takarar ne.

“Dukkanmu da muka gana babu wanda Buhari zai faɗi abu ya ce ba daidai ba ne…idan bai amince ba dole mu ajiye wannan magana tamu.”

Kazalika ya ce gwamnonin Kebbi da na Filato da na Nasarawa suka naɗa don su kai wa Buhari shawarar.

Game da janyewar tasa takarar, Gwamna Badaru ya ce ba zai iya janyewa ba sai abin da Buhari ya ce.

Leave a Reply

%d bloggers like this: