Sanata Ibrahim Shekarau ya ce ba zai yi ritaya daga siyasa ba har karshen rayuwarsa.

Shekarau ya sanar da haka lokacin da yake jawabi ga manema labarai bayan bude majalisar tuntuba ta Shura a Kano.

Shekaru wanda ya rike mukamin gwamna sau biyu, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nada shi a matsayin Ministan Ilimi gabannin zaben 2015.

Yanzu haka yana wakiltar Yankin Sanatan Kano ta Tsakiya.

Haka zalika, tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya karyata rahotannin da kafafen yada labarai ke yadawa cewa yana shirin kafa wata sabuwar jam’iyyar siyasa gabanin babban zaben 2023.

Obasanjo, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa ta fuskar yada labarai, Kehinde Akinyemi, ya fitar jiya, ya ce ba ya sha’awar siyasar jam’iyya a yanzu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: