Babban bankin Kasa na CBN yace yan Najeriya sun kashe sama da naira biliyan 100 kan ilimi a ƙasashen waje cikin watanni uku
Wata ƙididdiga daga Babban Bankin Najeriya wato CBN ta nuna cewa ƴan Najeriya sun kashe aƙalla dala miliyan 220.86 kan karatu a ƙasar waje daga Disambar 2021 zuwa Fabrairun 2022.
Hakan na nufin sun kashe sama da naira biliyan 100 a kuɗin Najeriya.
Jaridar Punch a ƙasar ta ruwaito cewa CBN bai bayyana adadin da yan ƙasar suka kashe a watan Maris da Afrilu da Mayu ba, inda bankin ya ce akwai yiwuwar adadin da ya fitar na daga Disambar 2021 zuwa Janairun 2022 a samu sauyi.
Ɓangaren ilimi musamman na jami’o’i a Najeriya na cikin wani hali sakamakon irin yajin aikin da malaman jami’o’i ke yi.