Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya zai kaddamar da kotun yanar gizo a gidajen gyaran hallaya da suke Najeriya

0 96

Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya Abubakar Malami SAN, zai kaddamar da Kotun yanar gido a gidajen gyaran hallaya da suke kasar nan wanda za’a rika sauraron kararraki ta Bidiyon kai tsaye.

Kakakin Ministan Dr Umar Jibrila Gwandu, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai.

A cewarsa, Ministan Shari’a Abubakar Malami, zai kaddamar da Kotun ne a gidan gyaran hallaya dake Kuje a Abuja.

Dr Gwandu, ya kara da cewa hakan yana cikin sauye-sauyen da Ministan ya kawo a fannin shari’a domin kawo karshen matsalolin da Fannin Shari’a yake fuskanta a Najeriya.

Kazalika, Sanarwar ta ce yin amfani da Na’urorin yana daga cikin Daftarin da Ministan kaddamar domin rage yaduwar cutar Corona a fannin Shari’a a watan Afrilu na shekarar 2020.

Leave a Reply

%d bloggers like this: