Kwamatin Lura da wurin da za’a gudanar da taron Jam’iyar APC na Kasa tare da Kawata shi, ya ziyarci dandalin Eagle Square da ke birnin tarayya Abuja a cigaba da shirye-shiryen taron Jam’iyar wanda ke tafe.

Shugaban Kwamatin kuma Gwamnan Jihar Plateau Simon Lalong, da ya ke Jawabi bayan duba wurin a ranar Juma’a a Abuja, ya ce ziyarar tana daga cikin shirye-shiryen taron Jam’iyar wanda ke tafe a sati mai zuwa.

Haka kuma ya ce Kwamatin ya na tattaunawa da sauran masu ruwa da tsaki da kuma Kungiyoyi domin tabbatar da cewa an sanya dukkanin abubuwan da ake bukata a wurin Kafin cikar lokacin taron.

Mista Lalong, ya ce Kwamatin sa, ya na aiki tare da Jami’an tsaro domin tabbatar da cewa an gudanar da zaben shugabannin Cikin Nasara ba tare da matsala ba.

Jam’iyar APC zata gudanar da taron ta na kasa a ranar 26 ga watan Maris din da muke ciki.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: