Babu tabbacin biyan albashi a kimanin jihohi 33

0 97

Babu tabbacin biyan albashi a kimanin jihohi 33 saboda matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na cire kudi daga asusun kananan hukumomi domin fara biyan naira biliyan 172 ga masu bayar da shawara kan mayar da kudaden bashi na Paris Cub, ya hada rigima tsakanin da jihohi da kananan hukumomi da kuma gwamnatin tarayya.

Wata kungiyar farar hula da ta himmatu wajen tabbatar da gaskiya a hada-hadar kudaden gwamnati, a cikin rahotonta ta ce gwamnatocin jihohi uku ne kawai da suka hada da Legas, Ribas da Akwa Ibom, za su iya biyan kudaden gudanarwarsu ba tare da tallafin gwamnatin tarayya ba.

An samu matsin lamba daga Kungiyar Gwamnonin Najeriya da sauran jama’a akan a dakatar da biyan kudaden ga masu bayar da shawarar.

Sai dai, a wani sauyin lamari mai ban mamaki, kasa da wata guda bayan umurnin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar, Ma’aikatar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsare ta kasa ta fara cire kudaden da za a biya masu bayar da shawarar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: