Babu wani cigaba da aka samu wajen kawo karshen yajin aikin gargadi da kungiyar ta shiga – Shugaban ASUU

0 61

Shugaban kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana cewa babu wani cigaba da aka samu wajen kawo karshen yajin aikin gargadi da kungiyar ta shiga.

Yajin aikin kungiyar wanda a yanzu ya shiga mako na 4, an fara shi ne sanadiyyar bukatun kungiyar na gyaran jami’o’in gwamnati na kasarnan da alawus-alawus na malamai tare da yarjejeniyar da kungiyar ta kulla tsakaninta da gwamnatin tarayya da kuma rashin daidaiton manjahar biyan albashi ta IPPIS.

Farfesa Osodeke, wanda ya bayyana a wani shirin gidan talabijin na Channels, ya bayyana takaicinsa kan abubuwan da suke faruwa da kuma gazawar gwamnati wajen cika alkawarukan da ta dauka shekaru biyu da suka gabata.

Shugaban ASUU ya koka bisa abinda ya kira shakulatun bangaro daga gwamnatin tarayya wajen kula da tsarin jami’o’in gwamnati, kasancewar za a iya biya musu bukatunsa a zaman ganawa tsakanin dukkanin bangarorin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: