Hukumar Lura da Kayyade Ayyukan Kamfanonin Samar da Wutar Lantarki ta Kasa, ta tabbatar da cewa Gwamnatin tarayya ta cire tallafin wutar Lantarki.

Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, shugaban Hukumar Malam Sanusi Garba, ya ce an aiwatar da hakan ne biyo bayan la’akari da tallafin da gwamnati ta ke bawa fannin fiye da shekaru, wanda aka sake yin Nazari a watanni 6 da suka gabata.

Hukumar ta bayyana hakan ne a lokacin da Najeriya ta ke cigaba da fuskantar matsalar karancin wutar lantarki, da man fetur da Gas da sauran su.

Malam Garba ya ce alhakin kamfanonin ne su sanar da abokan huldar su kan cewa gwamnatin tarayya ta cire tallafin da take bayarwa a wutar lantarki.

Kazalika, ya dora Alhakin saukar wutar lantarkin a kasa baki daya kan rashin kulawa da cibiyar samarda wutar akan lokacin kamar yadda aka tsara.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: