Bangarorin siyasa da ke gaba da juna na cigaba da kaddamar da zanga-zanga

0 58

An tsaurara matakan tsaro a Khartoum babban birnin kasar Sudan, yayin da bangarorin siyasa da ke gaba da juna suka kaddamar da zanga-zanga.

Daruruwan magoya bayan gwamnatin rikon kwarya ta Sudan sun bazama kan tituna, yayin da masu rajin goyon bayan sojoji ke cigaba da zaman dirshan a harabar fadar shugaban kasa, wanda suka fara ranar Asabar.

Sojoji da ‘yan sanda sun rufe hanyoyin zuwa helkwatar sojojin kasar.

Shugabannin bangarorin biyu sun yi kira ga magoya bayansu da kada su cakudu da juna, tare da tabbatar da kwanciyar hankali.

Yunkurin gwamnati Sudan na komawa mulkin farar hula tun bayan hambarar da Shugaba Omar al-Bashir a shekarar 2019 na fuskantar kalubalen siyasa da kabilanci da matsin tattalin arziki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: