Bankin CBN ya sanar da sabon adadin kudin da daidaikun mutane da kamfanoni za su iya fitarwa a banki

0 95

Babban Bankin Kasa CBN ya sanar da sabon adadin kudin da daidaikun mutane da kamfanoni za su iya fitarwa a banki, farawa daga ranar 9 ga watan Janairu mai zuwa.

Kamar yadda yazo a wata takarda da babban bankin ya aikawa sauran bankuna, dauke da sa hannun daraktan sanya ido a bankuna, Haruna Mustafa, babban bankin ya kayyade naira dubu 100 a matsayin kudin da daidaikun mutane za su iya fitarwa a banki ko POS cikin sati daya, da kuma naira dubu 500 ga kamfanoni cikin sati daya.

Sabuwar dokar ta kuma kayyade naira dubu 20 a matsayin kudin da daidaikun mutane za su iya cirewa a rana daga POS.

Takardar ta kara da bayyana cewa kudin da za iya cirewa ta ATM a mako daya kada ya haura naira dubu 100 da kuma naira dubu 20 a kowace rana.

Kazalika babban bankin ya sanar da cewa mafi girman takardar kudi da za a cire daga ATM kada ta haura naira 200.

Leave a Reply

%d bloggers like this: