Bankin Duniya ya bawa Najeriya dala miliyan 800 domin rage raɗaɗin tattalin arziki da talakawa ke ciki
Babban Bankin Duniya ya sake bayar da ƙarin kuɗade ga Najeriya a ƙarƙashin shirin National Social Safety Net Programme-Scale Up da aka ware dala miliyan 800 domin rage raɗaɗin halin tattalin arziki da talakawa ke ciki.
Binciken da jaridar The PUNCH ta gudanar ya nuna cewa adadin kuɗin da aka riga aka fitar ya karu daga dala miliyan 315 a shekarar 2023 zuwa dala miliyan 530 a bana, wanda ke nuna ƙarin kuɗi da aka shigar kwanan nan a asusun Najeriya domin wannan shiri na tallafi.
Ko da yake ba a iya tabbatar da takamaiman ranar da aka fitar da ƙarin kuɗin ba, rahotanni sun nuna cewa har zuwa ranar 30 ga Afrilu, 2025, Bankin Duniya bai sabunta bayanan da ke nuna ranakun ma’amala ba, wanda ke nuni da za’a fitar da kuɗin a cikin wannan watan.
Shirin dala miliyan 800 da aka amince da shi tun a ranar 16 ga Disamba, 2021, na da nufin bai wa mafi talaucin al’umma tallafi ta hanyar biyan su kuɗi kai tsaye, domin rage musu raɗaɗin cire tallafin fetur da sauran sauye-sauyen tattalin arziki.
Da farko dai, tsarin ya tanadi biyan naira dubu 5 a kowane wata ga kowanne gida da aka nufa. Sai dai sabbin manufofi da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta gabatar sun haɓaka wannan adadi zuwa naira 25,000 a kowane wata na tsawon watanni uku, da nufin tallafawa gidaje miliyan 15 a fadin ƙasar.