Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari.

Majiyoyi daga hukumar yaki da cin hanci da rashawa sun ce an kama tsohon gwamnan ne bisa zarginsa da hannu a badakalar naira biliyan 84 da tsohon Akanta Janar na Tarayya, Ahmad Idris ya yi.

An kama Yari ne da misalin karfe 5 na yammacin jiya bisa zarginsa da rabauta da Naira biliyan 22 daga cikin Naira biliyan 84 da tsohon Akanta Janar na Tarayya ya biya wani mai suna Akindele.

A cewar majiyoyin, hukumar ta kuma kama wani Anthony Yaro wanda shi ne shugaba kuma Manajan Darakta na kamfanin Finex Professional, kamfanin da ake zargin tsohon Gwamna Yari da hada baki da su wajan samun wasu karin kudaden.

Kamun tsohon Gwamna Yari ya zo ne kwana guda bayan da ya lashe tikitin tsayawa takara a jam’iyyar APC na daya daga cikin kujerun sanatoci uku na jihar Zamfara a majalisar dattawa ta kasa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: