Bayan kwashe watanni ana cece-kuce ministan shari’a Abubakar Malami zai tsaya takarar gwamna a jihar sa ta Kebbi

0 61

Bayan kwashe watanni ana cece-kuce, babban mai shigar da kara na Najeriya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami.

Ya tabbatar da cewa zai tsaya takarar gwamna a jihar sa ta Kebbi.

Malami ya bayyana hakan ne a dakin taro na fadar gwamnatin  jihar dake  Birnin Kebbi, babban birnin jihar, yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC wanda gwamnan jihar Atiku Bagudu ya halarta.

Ya ce ya amince kuma ya yanke shawarar tsayawa takarar ne sakamakon kiran da jama’ar jihar suka yi masa na ya tsaya takara.

Shuwagabannin jam’iyyar APC mai mulki a jihar, masu biyayya ga gwamnan jihar sun amince da sanarwar Malami.

Shugabancin jam’iyyar a jihar ya kasu kashi biyu ne masu biyayya ga Bagudu da kuma sauran masu biyayya ga tsohon gwamna Adamu Aliero.

Leave a Reply

%d bloggers like this: