Bayanai sun nuna cewa mutane 1,296 aka kashe a watan Mayu a sassan ƙasar nan

0 146

Wasu sabbin alƙalumma kan matsalar tsaro sun nuna cewa mutane 1,296 aka kashe a watan Mayu a sassan ƙasar nan.

Rahoton na kamfanin Beacon Consulting da ke nazarin tsaro a shiyyar Afirka ta yamma da yankin Sahel ya ce an samu ƙaruwar yawan waɗanda suka mutu a watan Mayu idan aka kwatanta da Afrilu inda aka kashe mutum 1,092.

Rahoton ya kuma ce mutane 1,086 aka yi garkuwa da su a sassan kasar a watan Mayu inda aka samu ragi idan aka kwatanta da watan Afrilu da aka yi garkuwa da mutane 1,178.

Rahoton Beacon Security and Intelligence Limited ya nuna cewa an samu ragi na kashi kusan shida cikin dari na matsalolin tsaro a Najeriya cikin watan Mayun da ya gabata, idan aka kwatanta da yadda lamarin ya kasance a watan watan Afrilu da ya gabace shi.

Rahoton ya nuna ce ragin da aka samu bai rasa nasaba da ƙoƙarin da jami’na tsaron ƙasar ke yi na yaƙi da matsalolin tsaro a sassan ƙasar. A hirarsa da BBC, shugaban kamfanin tsaron na Beacon Malam Kabiru Adamu ya ce akwai bukatar gwamnatoci a matakai daban-daban su fitar da tsarin da zai gaggauta rage talauci a tsakanin al.’umma, sannan a kyautata tsarin yaƙi da ta`addanci ta hanyar cusa al`umma a ciki, wato ta yadda za su dinga samar da bayanai ga jami`an tsaro da bangarorin da yaƙi da ta`addancin ya shafa.

Leave a Reply