Ƙaramin Ministan Tsaro, Dakta Bello Matawalle ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa sojoji biyar da ke bakin aiki a mahaɗar Obikabia da ke ƙaramar hukumar Obingwa a Jihar Abia, tare da alwashin cewa dole waɗanda suka aikata laifin su fuskanci hukunci.
Sojojin dai an kashe su ne a wani harin kwantan ɓaunar da wasu da ake zargin ƴan ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biafra ne ko reshensu na Eastern Security Network (IPOP/ESN), Matawalle ya ce kashe jami’an soji biyar da ba su ji ba ba su gani ba, abin takaici ne.
Cikin wata sanarwa da Daraktan ma’aikatar tsaro, Henshaw Ogubike, ya fitar ya ce waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki dole su fuskanci hukunci inda ya jajantawa iyalan wanda suka mutu da kuma sojojin Nijeriya, tare da karfafawa sojojin gwuiwa na kada su karaya saboda harin.
Ya kuma jaddada aniyar gwamnati na tallafa wa sojoji a ƙoƙarin da suke yi na fatattakar ƙungiyoyin IPOB da sauran masu tada ƙayar baya a wasu yankunan ƙasar nan don tabbatar da cikakken tsaro.