Shugaba Bola Tinubu ya aike da ta’aziyyarsa ga shugaban ƙasar Malawi kan rasuwar mataimakinsa, Saulos Chilima da wasu.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ya fitar, ta ce shugaba Tinubu ya jajanta wa iyalan mamacin kan wannan rashi da suka yi.
An samu jirgin saman da ke ɗauke da mataimakin ƙasar Malawi, ya yi hatsari kuma babu wanda ya tsira kamar yadda shugaba ƙasar, Lazarus Chakwera, ya bayyana.
Saulos Chilima da wasu mutum tara sun rasu a hatsarin jirgin saman da ya rutsa da su a ranar Litinin, wanda shugaba Lazarus Chikwera ya sanar a safiyar jiya Talata cewa hatsarin jirgin da Mista Chilima ke ciki ya yi ajalin duk wadanda ke ciki. Shugaba Chikwera ya ce, “jirgin ya yi karo ne da wani dutse, lamarin da ya yi sanadin tarwatsewarsa da mutanen ciki.” tun a ranar Litinin hukumomin kasar suka sanar da bacewar jirgin sojojin da ya dauko matakin shugaban kasar, inda nan take aka shiga lalube gano shi.