Buhari Da Tinubu Sun Taya Gwamnan Jihar Osun Adeleke Murnar Nasarar Da Ya Samu A Kotun Koli

0 164

A halin da ake ciki, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da hukuncin da kotun koli ta yanke kan zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar a ranar 16 ga Yuli 2022 da kuma muhimmiyar rawar da bangaren shari’a ke takawa wajen zurfafa dimokaradiyya da bin doka da oda.

Shugaban kasar ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar jiya a Abuja.

A cewar shugaba Buhari, bisa hukuncin kotun koli, babban aikin da ke gabansa a yanzu shi ne ganin jama’a su ji tasirin shugabanci nagari, inda jihar Osun za ta samu ci gaba, da dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Hakazalika, zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke murnar nasarar da ya samu a kotun koli, inda ya bukace shi da yayi gaggawar hada kan jihar.

Zababben shugaban kasar ya ce bisa hukuncin kotu mafi girma a kasar kan rikicin gwamnan jihar Osun, dole ne kowa ya mutunta hukuncin.

Leave a Reply