Wata kungiyar magoya baya ta sayi fom din takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC na naira miliyan 100 domin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan.

Wata majiya daga ofishin shugaban majalisar dattawa tace kungiyar ta sayi fom din a madadinsa a jiya a dakin taro na kasa da kasa dake Abuja.

Kungiyar tace za ta mika masa fom din ga Ahmad Lawan a gidansa dake Abuja.

A halin da ake ciki kuma, bulaliyar majalisar dattawa, Sanata Orji Kalu ya janye daga takarar neman shugaban kasa a zaben 2023 inda zai mara baya ga shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, domin maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023.

Orji Kalu ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya.

Orji Kalu ya soki masu neman takarar shugaban kasa daga sauran yankunan kudu bisa abinda ya kira rashin mutunta yankin Kudu maso Gabas da rashin adalchi a harkokin siyasa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: