Yan Nijeriyar da suka tsere zuwa Kamaru, dalilin ayyukan kungiyar BH, sun fara komawa gida a jiya Litinin, bisa radin kansu. Kashin farko da ya kunshi ’yan gudun hijira 5,000, wadanda suka kwashe shekaru 6 a sansanin Minawao dake Kamaru ne suka kama hanyar komawa gida a jiya cikin motocin bas. Continue reading
Kananan Labarai
Ana fargabar wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da ’yar uwar Ministar Harkokin Mata, Pauline Tallen a Jihar Filato. Aminiya ta samu cewa lamarin ya auku ne a unguwar Rantiya da ke yakin Dapit Karen na Karamar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar. Wani dan uwan wacce lamarin ya ritsa da ita, ya tabbatar wa wakilinmu […]Continue reading