CBN ya bawa bankuna umarni da su fara cire kashi 0.5 a duk lokacin da aka tura kuɗi ta asusun banki

0 177

Babban bankin Kasa CBN ya bai wa bankuna a ƙasar nan umarni da su fara cire kashi 0.5 cikin 100 a duk lokacin da aka tura kuɗi ta asusun banki a matrsayin kuɗaɗen tabbatar da tsaro ta intanet.

Cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Chibuzor Efobi, Daraktan kula da tsarin biyan kuɗi da Haruna Mustafa, Daraktan kula da manufofin kuɗi, babban bankin ya ce za a fara aiwatar da wannan tsari ne nan da makonni biyu masu zuwa.

A cewar CBN, kuɗin da za a cira domin tara harajin tsaron intanet ya zo ne sakamakon amincewa da dokar yaƙi da laifukan intanet ta 2024 da aka yi wa gyaran fuska.

Sanarwar ta ce za a zuba kuɗin da aka cira ne a asusun tsaron intanet na ƙasa wanda zai kasance a ƙarƙashin ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro.

Tsarin bai shafi masu karɓa da biyan bashi ba da kuɗaɗen albashi da kuma mutumin da zai tura kuɗi daga asusun ajiyarsa na banki zuwa wani asusun nasa na daban da kuma masu tura kuɗi zuwa wani asusun na banki ɗaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: