Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa ta ce kimanin mutane 64 ne suka harbu da cutar Corona

0 86

Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta ce kimanin mutane 64 ne suka harbu da cutar Corona a jiya a kasa baki daya.

NCDC ta ce an samu wanda suka harbu da cutar ne a jihohi 8 da suke kasar nan ciki harda birnin tarayya Abuja.

A rahoton na NCDC Kaduna ce mai mutane da yawa da suka harbu da cutar da mutane 23, sai Abuja 13 da Plateau 8.

Sauran Jihohin sune Bauchi (6), Lagos (5), Rivers (4), Bayelsa (2), Jigawa (2), and Kano (1).

A jiya an sallami mutane 74 da suka warke daga cutar a kasa baki daya.

Haka kuma a jiya an samu mutane 8 da cutar ta hallaka a Jihar Edo.

Kawo yanzu kimanin mutane dubu 212,829 ne suka harbu da cutar tun bayan bayyanarta, inda kuma a cikin su an samu mutane dubu 204,335 da suka warke, baya ga mutane dubu 2,914 da cutar ta hallaka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: