Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta ce kimanin sabbin mutane 519 ne suka harbu da cutar Corona a kasar nan baki daya.

NCDC ta ce an samu mutanen ne daga jihohi 14 da suke Najeriya ciki harda babban birnin tarayya Abuja.

Cibiyar ta NCDC ta ce kamar kullum Jihar Lagos ce akan gaba da mutane 120, sai Ogun 110 da kuma Rivers 74.

Sauran Jihohin sune Edo (63), FCT (58), Oyo (31), Kaduna (15), Bayelsa (11), Cross River (11), Delta (11), Kano (5), Ogun (4), Plateau (3), Adamawa (2) and Gombe (1).

Hukumar ta ce akalla akwai sabbin mutane 18 da suka mutu a sanadiyar kamuwa da cutar a jiha Talata, wanda hakan ya kawo adadin masu mutuwa a sanadiyar kamuwa da cutar zuwa dubu 2,637.

NCDC ta ce an kuma sallami mutane 292 bayan sun warke daga cutar.

Kawo yanzu kimanin mutane dubu 200,057 ne suka harbu da cutar tun bayan bayyanarta a kasar nan, cikin su kuma akwai mutane dubu 188,719 da aka sallama bayan sun warke daga cutar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: