Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta ce kimanin mutane dubu 2,339 ne suka harbu da cutar Kwalara, inda kuma a cikin su ta kashe mutane 74 daga Jihohi 30 na kasar nan cikin shekarar 2022.

NCDC a jiya Laraba ta ce yan kasa da shekara 5 maza da Mata sune cutar ta fi yiwa Illa cikin wannan shekarar.

Cibiyar ta bayyana sunayen Jihohin da abin ya shafa wanda suka hada da Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross River, Delta.

Sauran Jihohin sune Ekiti, Gombe, Imo, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ondo, Osun, Oyo, Plateau, Rivers, Sokoto, Taraba and Zamfara.

Hukumar ta ce kwamatin fasahar da ta kafa zai cigaba da aiwatar da aikin gaggawa domin sanin taimakon da cibiyar zata bawa Jihohin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: