Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta ce kimanin rahoton zazzabin Lassa 434 ta samu na a kasar nan cikin shekarar 2021.
Jihohin da abin ya shafa sun hada da Edo (192), Ondo (150), Taraba (21), Ebonyi (17), Bauchi (15), Benue (8), Plateau (8), Kaduna (7), Enugu (5), Nasarawa (3), Kogi (3), Cross River (1), Imo (1), Anambra (1), Delta (1), and Abia (1).
Cibiyar ta NCDC ta ce ta kuma samu rahotan cewa mutane 80 ne cutar Lassa ta kashe cikin shekarar nan.
NCDC ta ce ko a ranar Talatar nan sai da wata Mata mai juna biyu da wani Likita suka mutu a Jihar Nasarawa sakamakon cutar ta Lassa.
Haka kuma ta ce an samu wani Likita da shima ya harbu da cutar kuma yanzu hakan yana samun kulawar Likitoci a birnin tarayya Abuja.