Cibiyar NCDC ta tabbatar da cewa kimanin mutane 1,547 ne suka sake kamuwa da cutar corona

0 69

Cibiyar dakile bazuwar cututtuka ta kasa NCDC ta tabbatar da cewa kimanin mutane 1,547 suka kamu da cutar corona a jiya Litinin.

A cewar hukumar an samu sabbin mutanen da suka kamu da wannan cutar ne a Jihohin kasar nan 9 ciki harda babban birni  tarayya Abuja.

A jiyan an samu kimanin mutane (806) da suka kamu da wannan cutar a Abuja, sai jihar Lagos (401), Borno (166), Oyo (78), Ogun (47), Osun (30), Ekiti (7), Katsina (7), Kano (4), and Jigawa (1).

NCDC ta kara da cewa a jiyan an sallami kimanin mutane 193 bayan sun warke daga wannan cutar.

Ta kuma kara da cewa a ranar juma’a mutane 8 ne suka mutu sanadiyyar wannan cutar wanda ya mayar da adadin wadanda wannan cutar ta kashe zuwa 3,022.

Kawo yanzu dai adadin wadanda suka kamu da wannan cutar sun kai dubu dari 237 da 561 yayin da aka sallami mutum dubu dari 212 da 550 bayan sun warke.

Leave a Reply

%d bloggers like this: