Fadar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ce shugaban ƙasar lafiyarsa ƙalau bayan an samu rahoton cewa makusantansa sun kamu da cutar korona a ƙarshen mako.

Mai magana da yawun fadar Femi Adesina ne ya bayyana hakan lokacin da ya bayyana ta cikin shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels ranar Lahadi.

Da aka tambaye shi ko Buhari ya killace kansa, sai ya ce: “Ina ganin shugaban ƙasa lafiyarsa ƙalau, yana ci gaba da ayyukansa kamar yadda ya saba. Amma idan wani na kusa da shi ya kamu (da korona), zai killace kansa har sai ya warke. Saboda haka shugaban ƙasa yana ci gaba da ayyukansa kamar kullum.”

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: