Cristiano Ronaldo ya sake zama kan gaba cikin jerin ƴanwasan da aka fi biya a duniya.
Shekara uku a jere kenan ɗan wasan na Portugal na samaun wanann matsayi, da fitacciyar mujallar nan da ke ƙiyasin dukiya ta Fobes.Cristiano Ronaldo ya sake zama kan gaba cikin jerin ƴanwasan da aka fi biya a duniya.Cristiano Ronaldo ya sake zama kan gaba cikin jerin ƴanwasan da aka fi biya a duniya.
Mujallar ta ce sau biyar Ronaldo yana samun matsayin a sana’arsa ta ƙwallon ƙafa, inda ta ƙiyasta kudin da aka biya ɗan wasan da kimanin dala miliyan 275.
Adadi kudin da ɗan wasa ɗaya ne a tarihi ya taɓa zarta su, wato ɗan wasan dambe na duniya, Floyd Mayweathe, wanda a 2015 a ya samu kimanin dala miliyan 300.
A watan Disamban 2022, Ronaldo mai shekara 40 ya koma ƙungiyar Al Nassr ta Saudiyya a wani ciniki mai gwaɓin gaske.
Mujallar ta ce ɗan wasan ya samu kuɗi sakamakon wasu tsarabe-tsarebe da yarjejeniyarsa ta ƙunsa da kuma wasu tallace-tallace da kuma yawan mabiya a shafukansa na sada zumunta, da a yanzu suka kai miliyan 939.