Cutar Amai Da Gudawa Ta Kashe Akalla Mutane 10 A Kusa Da Pretoria Babban Birnin Kasar Afirka Ta Kudu

0 65

Cutar amai da gudawa ta kashe akalla mutane 10 a kusa da Pretoria babban birnin kasar Afirka ta Kudu, in ji hukumomin kiwon lafiya na kasar.

Ma’aikatar lafiya a lardin Gauteng ta Pretoria ta ce mutane 95 sun ziyarci wani asibiti wanda aka gano alamun kwalara da suka hada da gudawa, ciwon ciki da tashin zuciya.

Ma’aikatar cikin wata sanarwa tace, gwajin da aka yi a ranar Lahadi ya tabbatar da cewa akalla mutane 19 ne suka kamu sana diyyar cutar, inda ta kara da cewa mutane 37 na jinya a asibiti.

Wadanda abin ya shafa sun hada da yaro dan shekara uku da manya tara.

Nomantu Nkomo-Ralehoko, shugaban kula da lafiya na lardin, ya ce ana kara daukar karin ma’aikata da suka hada da likitoci da ma’aikatan jinya, domin shawo kan barkewar cutar.

Ana kamuwa da cutar kwalara ne ta hanyar gurbataccen abinci ko ruwa. Tun da farko, hukumomin birnin Pretoria sun bukaci mazauna Hammanskraal da kewaye  kada su sha ruwan famfo, bayan bullar cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: