Cutar amai da gudawa ta Kwalara ta kashe kimanin mutane 500 tare da harbar wasu mutane dubu 20 a jihar Jigawa

0 65

Cutar amai da gudawa ta Kwalara ta kashe kimanin mutane 500 tare da harbar wasu mutane dubu 20 a jihar Jigawa, daga watan Yuni zuwa Satumbar bana.

Sakataren zartarwar hukumar lafiya matakin farko ta jiha, Dr. Kabiru Ibrahim, ya sanar da haka a jiya yayin kaddamar da aikin rigakafin kwalara a karamin asibitin Baranda dake wajen Dutse, babban birnin jihar.

Yace aikin rigakafin wanda za a gudanar da hadin gwiwar ma’aikatar lafiya ta tarayya, an fito da shi ne da nufin dakile bazuwar cutar.

Kabiru Ibrahim yace jihar Jigawa ta samu alluran rigakafin kwalara guda miliyan 1 da dubu 400 kuma hukumar tana sa ran yiwa yara dubu 720 allurar rigakafin yayin aikin.

Yayi bayanin cewa duk wanda ya cancani ayi masa rigakafin yana bukatar ayi masa allurar sau 2 cikin watanni uku.

Yace za a gudanar da aikin rigakafin a Kananan Hukumomi 3 na Dutse da Birnin Kudu da Hadejia.

Leave a Reply

%d bloggers like this: