Wata Jami’ar ma’aikatar lafiya ta tarayya, Salma Kolo, ta ce cututtukan da ke da nasaba da juna biyu sun fi kashe mutane a Najeriya fiye da kwayar cutar Corona mai saurin kisa.

Dr. Salma Kolo, wacce ita ce Daraktan Kula da Lafiyar Iyali a Ma’aikatar, ta bayyana hakan ne a yayin wani horo na kwanaki uku na kafafen yada Labarai wanda kungiyar Rotary ta shirya.

Ta ce akalla mata dubu 40 ne a Najeriya suke rasa rayukansu a duk shekara sakamakon matsalolin da suka shafi juna biyu da haihuwa.

Ta yi nuni da cewa sama da yara miliyan daya ‘yan kasa da shekaru biyar sune suke mutuwa sakamakon rashin iyayensu mata wanda suka mutu a lokacin haihuwa.

Salma Kolo ta ce domin kawo karshen wannan matsalar yana da kyau mata musamman mazauna karkara su rungumi tsarin iyali.

Ta ce ya kamata mata su rungumi tsarin iyali ba wai a matsayin hanyar rage yawan al’ummar kasar ba, sai dai a matsayin wata hanya ta inganta rayuwarsu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: