Da Alama Ana Samun Nasarar Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Kasar Sudan

0 78

Da alama ana samun nasarar yarjejeniyar tsagaita wuta a kasar Sudan bayan yarjejeniyar ta fara aiki da karfe sha biyun dare agogon kasar.

Wannan dai shi ne yunkuri na hudu na dakatar da fadan da aka fara a ranar 15 ga Afrilu, ba tare da an samu nasarar aiwatarwa ba.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta sa’o’i 72 tsakanin sojojin kasar da kuma dakarun RSF bayan shafe sa’o’i 48 ana tattaunawa.

An samu labarin wasu harbe-harbe a yau a Khartoum babban birnin kasar.

An kuma samu rahotannin jiragen yaki na shawagi a sama, amma fararen hula na komawa kan titunan babban birnin kasar.

Bangarorin biyu da ke rikicin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 400, sun sanar da amincewa da yarjejeniyar tsagaita wutar.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya yi gargadin tashin hankalin da ake yi a Sudan zai iya mamaye yankin baki daya da ma sauran yankuna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: