Da gaske ne gwamnoni jihohi na danne kuɗin ƙananan hukumomi a cewar ALGON

0 59

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta Najeriya, Hakeem Ambali ya ce kalaman shugaban ƙasar Muhammadu Buhari kan cewa gwamnoni na danne wa ƙananan hukumomi gaskiya ne.

Jaridar Punch ta ruwaito Ambali na cewa “ana facaka da kuma danne kuɗaɗen ƙananan hukumomi.” Muna son shugaba Buhari ya yi ta-maza ya magance wannan matsala.

Ya ƙara da cewa “idan ana so a magance matsalolin talauci da rashin tsaro, to dole ne a bai wa ƙananan hukumomi cin gashin kansu.”

Daga nan sai ya buƙaci shugaban ƙasar da ya tursasa gwamnoni su sanya hannu kan dokar cin gashin-kai na ƙananan hukumomi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: