Dakarun Operation Hadin Kai cikin sati 2 da suka gabata sun kashe yan ta’adda 14 tare da kama wasu 15

0 84

Ofishin Hukumar Tsaro na Kasa ya ce dakarun Operation Hadin Kai, cikin sati 2 da suka gabata sun kashe yan ta’adda 14 tare da kama wasu 15.

Da yake zantawa da manema labarai, Daraktan Yada Labarai na Ofishin Mr Bernard Onyeuko, ya ce hakan ya biyo bayan wasu sabbin hare-hare da sojojin suka gudanar a yankin Arewa maso Gabas a tsakanin 19 ga watan Mayu zuwa 2 ga watan Yuni.

Mista Onyeuko, ya ce Sojojin sun kubutar da Iyalai 100 wanda suka kunshi Mata 33 da kuma Yara 67 wanda yan ta’addar suka sa ce.

Haka kuma ya ce a ranar 22 ga watan Mayu ne rundunar ta ragargaji yan ta’addar a yankunan Amdaga, Balazola, Ndakaine, Jango, Sabah da Gobara ta karamar hukumar Gwoza ta Jihar Borno.

Kazalika, ya ce dakarun su, sun kori mayakan ISWAP da Boko Haram daga maboyarsu a lokacin aikin atisayen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: