Dakarun sojin Najeriya suka kubutar da wasu mata 18, da aka yi garkuwa da su

0 183

A ranar Larabar da ta gabata ne dakarun sojin Najeriya suka kubutar da wasu mata 18, da aka yi garkuwa da su, tare da mika su ga gwamnatin jihar Katsina.

Kwamandan runduna ta 17 ta Sojojin Najeriya, a jihar Katsina, birgediya Janar Oluremi Fadairo, shine ya bayyana hakan ga manema labarai, inda ya ce sojojin sun kai wani samame ne a yankin ‘yan ta’addan da ke dajin Yan-Tumaki da Dan-Ali.

A cewarsa, sojojin sun yi artabu da ‘yan ta’addan, inda suka yi nasarar kubutar da wadanda aka sacen.

Da yake mika wadanda lamarin ya rutsa da su ga kwamishinan tsaro, da harkokin cikin gida na jihar Katsina Dr Nasiru Mu’azu, kwamandan ya jaddada shirye-shiryen rundunar sojin Najeriya, na ci gaba da kokarin maido da zaman lafiya na dindindin a jihar.

Kwamandan ya umurci jami’an da ke karkashin rundunar da su ci gaba da gudanar da irin wannan aikin ceto, domin ganin an kubutar da sauran wadanda aka yi garkuwa da su. Da yake mayar da martani, Mu’azu ya jaddada kudirin gwamnati na maido da zaman lafiya a jihar ta katsina ga baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: