Dalar Amurka ($) na faɗuwa a kasuwannin canjin kuɗaɗe ta kasar nan daga N940 zuwa N890

0 379

Farashin dala na faɗuwa a kasuwannin canjin kuɗaɗe ta kasar nan daga naira 940 zuwa naira 890 a safiyar yau Laraba kamar yadda bayanan da Sawaba radio ta samu daga kasuwannin canji a birnin Legas da ke kudancin ƙasar nan suka nuna.

Bayanan sun nuna cewa a safiyar jiya Talata, an sayar da dalar kan naira 940, da yamma kuma, ta fadi zuwa naira 927 a kasuwannin canjin a Legas.

Wannan na zuwa ne bayan ganawa da muƙaddashin gwamnan babban bankin kasa, Folashodun Shonubi, ya yi da shugaba Bola Tinubu a ranar Litinin a fadarsa da ke Abuja, kan yadda za a farfaɗo da darajar Naira.

A kasuwannin canji na Abuja kuma, a safiyar yau Laraba, dalar ta fadi zuwa naira 900, inda a safiyar jiya Talata, aka sayar da ita kan naira 947, da dare kuma, ta sauka zuwa 910.

Haka ma a jihar Kano, bayanai daga kasuwannin canji na nuna cewa dalar ta faɗi daga naira 946 a safiyar jiya Talata zuwa naira 900 a safiyar yau Laraba.

A daren jiya dalar ta fara sauka a kasuwannin canji na Kano inda ta sauka zuwa naira 927. Wannan lamari na nuna cewa darajar kuɗin naira ta fara farfadowa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: