Daliba mace ta farko dake koyon ilmin tukin motar hakar kasa a Sin

0 169

Bisa karuwar matsayin mata, yanzu mata da yawa suna gudanar da ayyukansu, har ma suna taka muhimmiyar rawa kan ci gaban al’umma. Amma, a ganin mutane masu yawa, wasu ayyuka kamar masu kashe gobara, mahauta, da masu ilimin kasa da dai sauransu, ya kamata a ce maza ne za su yi su, wadanda kuma ake kiransu “aikin maza”.

A hakika dai, wannan ra’ayin jinsi ne da aka saba nunawa, wanda kuma ke wanzu a cikin al’umma. Amma me ya sa zamu iyakance jinsin wadannan ayyukan? Amma, me ya sa aka kayyade wadannan ayyuka bisa jinsi? Ko mata ba za su iya yin abin da maza suke iya yi ba ne? tabbas ba haka ba ne.

Bai kamata a kuntata aikin mata, ko kuma a nuna bambanci a shekarunsu na haihuwa ko jinsi ba. Matan da suka yi fice mafi yawa, sun soma fita daga iyali zuwa al’umma domin gudanar da ayyukansu, kuma ayyukan da suke iya zaba suna kara karuwa, wannan ne kuma girmamawa da tabbacin da ya kamata al’umma ta ba su.

Dangane da jerin bayanan da Ofishin kididdiga na kasar Amurka ya fitar, an nuna cewa, jimillar yawan ma’aikata na kasar Sin da yawan ma’aikata masu karfi duk sun kasance mafi girma a duniya. Daga cikinsu, yawan matan da ke aikin ya kai kimanin kashi 70%, wanda ya kai matsayi na farko a duniya. Amma, a cikin rahoton jerin sunaye kan gibin dake kasancewa tsakanin jinsi na shekarar 2017 da Dandalin Tattauna Tattalin Arzikin Duniya ya fitar, matan kasar Sin sun kasance a matsayi na 100 cikin kasashe 144 a duniya. Wannan matsayin yana da ban mamaki. Ana iya ganin cewa, matan kasar Sin sun fi kokari idan an kwatanta da maza wajen gudanar da ayyukansu. To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku wani bayani game da wata yariniya, wadda take koyon tukin motar hakar kasa a makarantar koyon fasahohin sana’o’i.

Han Linlin, daliba ce ta farko dake koyon ilmin tukin motar hakar kasa a garin Dongxiang na gundumar Linxia ta lardin Gansu dake arewa maso yammacin kasar Sin.

Game da dalilin da ya sa ta tsaida kudurin koyon yadda ake tukin motar hakar kasa, Han Linlin ta ce,

“Ko shakka babu, ina sha’awar tukin motar hakar kasa, tun lokacin da nake karama, dabi’una kamar na da namiji ne. Don haka, ayyukan da mata suke son yi, ni ba na so, ko kuma ba zan iya yi sosai ba.”

Han Linlin ta gaya min cewa, a ‘yan shekarun da suka gabata, ta fita zuwa ci raini, daga baya sai ta yi muradin koyon wata fasaha, wadda take sha’awa kuma ke iya taimake mata wajen samun kudin shiga. A cewarta, ko da yake iyalinta basa fama da talauci, tana fatan rage nauyin dake wuyan iyayensu.

Mahaifin Han Linlin yana aiki ne a wani wurin gine gine, mahaifiyarta ba ta aiki sai zaman gida domin kulawa da iyali, kanwarta tana karatu a makarantar firamare, kaninta daya kuma na gidan renon yara. Ta ce,

“Yanzu, kudin shigar da nake samu a ko wane wata, ya kai a kalla dubu 6, adadin da ya ke matsayin gaba a gundumar Dongxiang. Ina amfani da kudi kadan, sannan na kan sayowa kannena wasu abubuan karatu, saura kuma sai in baiwa iyaye na, domin rage musu nauyin.”

Kamar yadda aka sani, irin aikin tukin motar hakar kasa, aiki ne mai wahala, ko shakka babu idan ana fatan samun ilmin yadda ya kamata, dole ne a kara kokari sosai. Kuma idan ana gudanar da irin aiki, to ba zai yiwu a sanya tuffafi masu tsabta da kuma kyan gani ba, game da haka, Han Linlin ta gaya min cewa,

“Muna koyon fasahar har na tsawon sa’o’i 8 a ko wace rana. Gaskiya na sha wahala, amma idan ba a sha wahala ba, to ba za a iya samun wannan fasaha sosai ba. Idan ina iya samun kudin shiga, da zan taimakawa iyalina su kyautata zaman rayuwarsu, da kuma faranta musu rai, to, sanya tuffafi da kayan ado masu kyau ko a’a, ba abun damuwa ba ne.”

Han Linlin ta ce, da farko, iyayenta ba su yarda da ta zo nan domin koyon ilmin tukin motar hakar kasa ba.

“Ba su yarda ba, saboda a ganinsu, wannan aiki ne mai hadari. Amma, ina son wannan aiki sosai, na fada musu cewa, idan ana tsoron hadari, to ba za a iya yin kome yadda yakamata ba. bayan ganin niyyata ta koyon fasahar, sai mamata ta ce, “to sai ki je ki koya tun da kina so. ”

A cikin wannan makatantar koyon fasahohi a fannin sana’o’i, yawancin dalibai sun fito ne daga gundumar, kuma galibinsu dalibai maza ne. Saboda aikin tukar motar hakar kasa na bukatar karfi sosai, don haka na tambaye ta ko akwai yiwuwar tana ji ba ta kai dalibai maza kokarin koyon fasahar ba, Han Linlin ta amsa cewa,

“Ba zai yiwu ba, ko da yake dalibai maza su kan yi min wasa cewa, ba za ki iya ba, sauka sauka daga motar, amma a hakika dai sun amince da karfi na na koyon fasahar.”

Daliba ce ta farko dake koyon ilmin tukin motar hakar kasa a garin Dongxiang_fororder_微信图片_20210303121028

Daliban maza na ajinsu sun kuma yabawa karfin karatu irin na Han Linlin,

“Lallai tana tuka motar hakar kasa cikin sauri, kuma tana koyon fasahar cikin sauri, yawancin ‘yan mata su kan ji tsoron koyon wannan, amma ita ba haka take ba, har ma a wasu lokuta ta fi mu iya tukin motar.”

A karshe dai, Han Linlin ta ce, tana koyon fasahar tukin motar haka kasa a nan ne ba tare da biyan kudi ba, ko a fannin karatu ko a fannin wajen kwana ko kuma a fannin cin abinci. Ban da wannan kuma, a gabannin kammala karatu, makarantar za ta taimake musu wajen neman aikin yi.

Garin Dongxiang na gundumar Linxia ta lardin Gansu dake arewa maso yammacin kasar Sin, ya taba fama da talauci sosai. Kamar yadda Sinawa kan ce, “Koya wa mutane yadda ake kamun kifi ya fi ba su kifi kai tsaye”. Domin fitar da mazauna wurin daga kangin talauci, garin nan yana ta bin ra’ayin “Dora muhimmanci kan ba da ilmi da fasahohi domin kawar da talauci”.

A cikin ‘yan shekarun nan, makarantar tana kara kokarin ba da horo a sana’o’i daban daban guda 12, ciki har da gasa kek irin na kasar Sin, walda na wutar lantarki, aikin wutar lantarki, kwaliya da aski, tukin motar hakar kasa, jigilar kayayyaki da dai sauransu. A karkashin goyan baya daga hukumomi daban daban na gwamnatin wurin, makarantar ta bada tabbacin ganin dalibai sun koyi fasahohi sosai, wadanda za su amfanesu a nan gaba, da nufin cimma burin samun ayyukan yi, da kara samun kudin shiga ta hanyar samun fasahar da aka koya, ta hakan ake inganta ayyukan koyar da sana’o’i cikin sauri.

Asalin labarin:

http://hausa.cri.cn/20210303/6eb3d5aa-c22c-f17f-5d8a-b5d5406922c6.html

Leave a Reply

%d bloggers like this: