Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta sake kama tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode bisa zarginsa da amfanin da takardun bogi.

An kama Fani-Kayode ne a jiya bayan kammala shari’a a babbar kotun tarayya da ke Ikoyi a Legas.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an hukumar sun kama tsohon ministan ne, bayan da alkalin kotun, Daniel Osaigor, ya dage ci gaba da sauraron shari’ar da ake yi kan badakalar kudi naira miliyan dubu hudu da miliyan 900.

An rawaito cewa an kai shi ofishin hukumar nan take.

Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya ci tura.

Da aka tuntubi mai magana da yawun Fani-Kayode, Gloria Nzenwa, ta ki cewa uffan dangane da batun.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: