Tsohon gwamnan jihar Jigawa Ibrahim Saminu Turaki a jiya ya koma jam’iyyar PDP inda ya kawo karshen zamansa a jam’iyyar APC mai mulki.

Saminu Turaki ya koma PDP ne tare da jiga-jigan ‘yan siyasa na jam’iyyar APC ciki har da tsohuwar kwamishiniyar harkokin mata a jihar, Ladi Dansure.

Tsohon gwamnan ya shaidawa manema labarai a gidan sa na Kano cewa ya koma jam’iyyar PDP ne domin ciyar da jihar Jigawa gaba, da kuma ‘yantar da jama’a daga mulkin kama-karya na jam’iyyar APC.

Sai dai an samu labarin cewa Saminu Turaki ya fito takarar Sanatan Jigawa ta Arewa maso Yamma.

Wani mai neman kujerar a karkashin jam’iyyar PDP, Nasiru Umar Roni, ya janye masa.

A nasa jawabin, shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Babandi Gumel, ya ce tsohon gwamnan ya koma PDP ne tare da dubban magoya bayan sa.

Ya ce Saminu Turaki ya samu tarba daga dukkan iyalan jam’iyyar PDP a jihar Jigawa ciki har da tsohon gwamna Sule Lamido.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: