Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aika da tawaga ta musamman zuwa jihoshin Sokoto da Katsina sakamakon yadda ‘yan bindiga ke cigaba da kai hare-hare a yankunan jihohin.

Mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya sanar da hakan inda ya ce shugaban kasar yana jiran rahoto cikin gaggawa da kuma shawarwari kan matakin da ya kamata a dauka domin magance matsalolin da jihohin ke fuskanta.

Cikin wadanda Buharin ya tura akwai babban mai ba shi shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya da Sufeto Janar na Yansanda Usman Alkali Baba da daraktan hukumar tsaro ta farin kaya DSS Yusuf Magaji Bichi da daraktan hukumar tattara bayanan sirri ta kasa Yusuf Magaji Bichi da kuma shugaban tsaro na rundunar sojin Najeriya Manjo Janar Samuel Adebayo.

Wannan matakin dai na zuwa ne jim kadan bayan yan kasar da dama sun nuna bacin ransu kan kasashe-kashen da ake kara samu da garkuwa da mutane a kasar.

Ko a yau ma sai da wasu suka fita zanga-zanga a wasu sassan kasarnan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: