Dalilan da yasa shugaba Buhari ya dakatar da cire tallafin man fetur

0 80

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da shirin cire tallafin man fetur har sai abinda hali yayi.

Karamin ministan man fetur, Timipre Sylva, ya sanar da haka ga manema labarai a jiya bayan ganawa da shugaban kasa.

Ministan ya kara da cewa bangaren zartarwa na shirin mika bukata ga majalisun kasa akan karin watanni 18 na fara aiwatar da dokar man fetur ta PIA wacce aka shirya fara aiwatarwa a watan Fabrairu mai zuwa.

Tunda farko an shirya cire tallafin man fetur a watan Yunin bana.

Shugaba Buhari a ranar 16 ga watan Augusta na 2021 ya sanya hannu akan kudirin dokar man fetur bayan majalisar dattawa da ta wakilai sun zartar da ita a watan Yulin bara.

Ana sa ran dokar man fetur ta PIA za ta karfafa gwiwar masu zuba jari a bangaren masana’antar man fetur tare da samar da damarmakin ayyuka domin jama’ar dake rayuwa a guraren da ake hakar man.

Leave a Reply

%d bloggers like this: