Wasu tsoffin yan Majalisar Jiha dana tarayya a lokacin gwamnatin Sule Lamido, sun fice daga Jam’iyar PDP zuwa Jam’iyar NNPP.

Shugaban Jam’iyar NNPP na rikon Kwarya Musa Bako Aujara, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan gama taron masu ruwa da tsaki a Ofishin Jam’iyar da ke Dutse.

A cewarsa, tsoffin Kwamishinonin, da yan Majalisar Jihar da kuma magoya bayan su, sun fita daga Jam’iyar PDP zuwa NNPP saboda karfa-karfar Jam’iyar PDP da kuma rashin sanin inda ta dosa.

Hon Aujara, ya ce Jam’iyun PDP da APC sun gaza ta kowacce fuska, biyo bayan yadda suka kasa ciyar da kasar nan gaba tare da kyautatawa Talakawa.

Haka kuma ya ce yan Najeriya sun gaji da karerayin APC da PDP, inda ya ce Jam’iyar NNPP ce kadai mafita ga yan Najeriya.

Kazalika, ya ce Jam’iyar NNPP ta yi wani shiri na karbe iko daga hannun Jam’iyar APC a shekarar 2023.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: