Sakamakon bana ya nuna irin yadda aka ƙara inganta yanayin rubuta jarabawar yadda ya kamata.
Ministan Ilimi a Nijeriya, Tunji Alausa ya ce hana satar amsa ne ya janyo faɗuwar ɗalibai a jarawabar shiga manyan makarantu ta JAMB a bana.
Ya ce sakamakon bana da aka samu, ya nuna irin yadda aka ƙara inganta yanayin rubuta jarabawar yadda ya kamata.
Ya bayyana cewa hakan kuma ya nuna yadda tsarin rubuta jarabawar ya daƙile satar amsa da ɗalibai ke yi.
A ranar Litinin ne JAMB ta fitar da sanawar fitar da sakamakon bana tana mai cewa yawancin ɗaliban da suka zauna jarabawar sun gaza samun maki 200 daga cikin maki 400.
JAMB ta ce ɗalibai miliyan 1.95 ne suka rubuta jarabawar, amma cikin wannan adadi, miliyan 1,534,654 ne wanda ya kai kaso 78 cikin 100 suka samu maki ƙasa da 200.
Alƙaluman sakamakon ya nuna cewa kashi 0.63 ne na ɗalibai ƙalilan da suka samu makin da ya haura 300, wanda a jimlace suka kai ɗalibai 12,414.
A matakin maki tsakanin 250 zuwa 299 kuma, an samu ɗalibai 73,441 yayin da ɗalibai 334,560 suka samu maki tsakanin 200 zuwa 249.