Dalladi Auyo: Na bar jam’iyar APC zuwa NNPP saboda zagon kasan da akemin

0 107

Wani Jigo a Jam’iyar APC ta Jihar Jigawa Alhaji Danladi Auyo, ya bar Jam’iyar zuwa Jam’iyar NNPP.

Wani Jigo a Jam’iyar ta NNPP kuma tsohon Mataimaki na musamman ga Sule Lamido, Muhammadu Lawan Kazaure, shine ya bayyana hakan cikin wata tattaunawa ga manema labarai a Dutse.

A cewarsa, Danladi Auyo ya shiga Jam’iyar NNPP ne tare da magoya bayan sa, inda ya ce kofar Jam’iyar a bude take ga masu sha’awar shigowa.

Manema Labarai sun rawaito cewa kimanin watanni 6 da suka gabata ne Jam’iyar APC ta dakatar da Danladi Auyo saboda zargin yiwa Jam’iyar zagon kasa.

An bada rahotan cewa Danladi Auyo, ya shiga Jam’iyar NNPP ne domin ya tsaya takarar Sanatan Jigawa ta Gabas.

Leave a Reply

%d bloggers like this: