Damodi ya jaddada kudurin inganta harkar ilimi, ta hanyar bai wa ‘ya’ya mata damar samun ilimi mai nagarta.
Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na inganta harkar ilimi, musamman ta hanyar bai wa ‘ya’ya mata damar samun ilimi mai nagarta.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen bikin kaddamar da rabon rigunan makaranta kyauta guda dubu 30 ga dalibai mata, da kuma kayan wasanni ga manyan makarantun sakandare a fadin jihar, wanda aka gudanar a makarantar sakandiren kimiyya tayanmata da ke Jahun.
A cewarsa, tallafa wa ‘ya’ya mata wajen samun ilimi na daga cikin muhimman manufofin gwamnatin sa, domin hakan na da matukar tasiri wajen gina al’umma mai wayewa da ci gaba.
Gwamna Namadi ya bayyana cewa wannan shiri na daga cikin manufofin da gwamnati ke aiwatarwa na samar da ilimi kyauta ga ‘ya’ya mata tun daga matakin firamare har zuwa jami’a.
Ya kara da cewa gwamnatin sa ta tanadi tsare-tsare na musamman don gano dalibai mata masu hazaka da kuma tallafa musu wajen karatun likitanci da sauran bangarorin lafiya, domin cike gibin da ke fagen kula da lafiya a yankunan karkara. A karshe, Gwamna Namadi ya ce an zuba biliyoyin naira wajen gyaran makarantu, horas da malamai da kuma sayen kayan koyarwa domin inganta yanayin koyo da koyarwa a jihar